10 Maris 2019 - 17:34
Wani Jirgin Ethiopia Ya Yi Hadari

A yau ne wani jirgin saman fasinja na kamfanin Ethiopian Airlines, kirar Boeing 737 ya fadi dauke da fasinjoji 149, da ma'aikatansa 8.

Jirgin ya fadi ne muntina shida bayan tashinsa a safiyar yau Lahadi daga birnin Addis Ababa na kasar Habasha zuwa birnin Nairobi fadar mulkin kasar Kenya.

Mahukuntan kasar Habasha sun sanar da cewa dukkanin mutanen da suke cikin jirgin sun rasa rayukansu, wadanda suka hada da 'yan kasar ta Habasha, da kuma 'yan wasu kasashe daban-daban.

Tuni Pira ministan kasar ta Habasha, Abiy Ahmed, ya aike da sakon ta'aziya ta shafinsa na twitter ga iyalen wadanda hatsarin jirgin ya yi ajalin su.